。
Da_MEYE GASKIYAR LABARIN TSAKA DA CUTUKKAN DA TAKE JANYOWA ? KO DA GASKENE TANA HAIFARDA GOBARA ?_*
:
_*AMSA :*_
:
_Ita dai wannan halitta mai suna tsaka tayi kama da kadangare amma kuma ba kadangaruwa bace,tana rikida da launi daban daban kamar yanda kuke gani a hoto.Tana da wutsiya mai kauri wanda anan ne take tara kitse waton (fat) wanda ke zama a matsayin abinci a gareta a sanda bata da lafiyar zuwa kiwo ko iya kaiwa ga wajen da zata ci abinci,to wannan kitsen dake a cikin wutsiyarta,shi za tayi amfani dashi a matsayin abinci._
_Tana somawane da kwai masu dimbin yawa(lays a number of eggs) har ta kenkeshe kwayakwan wanda wannan yassa ake ganinta da yawa a cikin gida._
_Ta kasance daya daga cikin halittunda kusan a kowace kasa ta duniya akan sameta,kama daga kasashen Larabawa,kasashen Turawa,India da kuma nahiyar kasashen bakaken fata waton African continent._
_Tun a zamanin Manzanni,wannan halittar takasance abin qyama,abin gudu da ake yiwa barazanar kashewa a duk sanda aka ganta._
_To ko me ya janyo haka ?_
_Addinance,an umurce mu da a duk inda muka ga tsaka to mu kasheta domin fadar manzon Allah (s.a.w) a hadisin da Abu Hiraira ya ruwaito mai cewa "DUK WANDA YA KASHE TSAKA DA BUGU GUDA TO YANA DA LADA SABA'IN" [Muslim]._
_Amir bn Sa'ad ya ruwaito daga mahaifinsa wanda yake cewa Manzon Allah (s.aw) yayi umurni da a kashe tsaka[Muslim]._
_Saeed Ibn Almusayyib ya ruwaito cewa Umm Shareek ya gaya masa cewa Manzon Allah (s.a.w) ya umurce shi da ya kashe tsaka[Albukhari da Muslim]_
_Akwai hadisin da ya ruwaito cewa tsaka ita ce halittar data hura wutar da kafurrai suka jefa Annabi Ibrahim (a.s) a cikinta.Tayi hakan ne dan kara zafin wutar._
_Duk da yake wasu na ganin wannan hadisin bai inganta ba domin ba hadisi bane da aka ruwaito daga bakin ma'aiki sai dai an ruwaito shi ne daga Ibn Jurayi._
_A hakika duk abinda munka ga Ma'aiki ya umurcemu da mu kashe idan mun ganshi to barinshi a raye na iya zamowa wani hadari na daban,domin idan mun duba zamu ga ai akwai dubban halittu amma kuma kadan daga cikinsu ne muka san ana kashewa don lahanin da suke da shi ga lafiyar al'umma.Sai ga wannan halittar wanda kasheta ma nada lada,wanda wannan na janyo hankullanmu na a duk inda munka ganta to muyi gaugawan kasheta._
_A al,adance an camfa wannan halittar inda wasu magangannu ke karo da juna.Wasu kuma ke ganin duk abinda aka fada akan wannan halittar to a hakika gaskiya ne._
_Ga kadan daga cikin magangannun da naga suna ta yawo a shafin sada zumunta akan wannan halittar mai suna 'tsaka' wanda a hakika akwai camfi a cikin labaran sosai da kuma yin imani da abu har yakasance yana da lahani(waton belief)_
_Idan aka bar garin abinci a bude to zata shiga a cikin garin ta yi birgima a ciki idan aka yi abinci da garin to sai a kamu da cutar kuturta ko miyagun kuraje._
_Idan aka bar ruwa a bude ta shiga a ciki to takan yi fitsari a cikinsu tayi kashi sai ta fita idan aka sha ruwan za a kamu da mummunar cutar da bata da magani._
_Idan ta shiga a cikin abinci to idan aka ci abincin za a kamu da ciwon shanyewar bangaren jiki._
_Tsaka tana haddasa gobara idan ta gawurta._
_Tsaka idan taiyi tsartuwa a cikin ruwa to takan haifarda miyagun kuraje a cikin baki dana fata wadanda za a rasa maganinsu._
_Wadannan kadanne daga cikin magangannu da naga suna yawo a kafar sada zumunta (social media),_
_abinda zan iya cewa anan shi ne wasu magangannun camfe camfene kawai na al'adu na yau da gobe ,domin kimiyance babu wannan binciken da ya lisafo tsaka na haddasa miyagun cutukkan da basu da magani ba.Akwai kasashen da suke kallonta kamar yanda muke ganin kadangare.Akwai kuma kasashen da suke kallonta a matsayin munafukar halitta mai kama da dabi'un yahudawa._
_Zan kuma iya iyarda da idan ta gawurta tana haddasa gobara domin anan idan mun duba halitta ce da take tafiya kama da na iska tana yi tana canza launin fata da sura kuma gata evil ce._
_So da dama mukan yi karo da ruwan da tasha ko abincin da ta shiga a ciki amma kuma saboda bamu sani ba sai Allah ya karemu daga duk sharrin wata cuta da ake iya dauka ga abinda ta ci ko ta sha._
_Amma a duk sanda mun kayi imani da cewa dazaran kaci ko ka sha sauran tsaka to lallai zaka kamu da cuta to wannan na iya shafuwarka(belief and myth kenan)_
_Kimiyance wadanne cutukkane take kawowa ?_
_Akwai likitan da akayiwa tambaya akan tsaka mai suna "ARINKAWA ADEOLU,federal medical center, Jabi, Abuja wanda yace "zama da tsaka na haddasa yiwuwar kamuwa da zazza6in Typhod"_
_Shi ko Adeolu ya gayawa News Agency,Nigeria cewa "tsaka tana dauke da Salmonella typhi waton wasu qwayoyin cutane na bacteria dake janyo typhod fever._
_Wadannan kwayoyin suna nan a cikin kashinta da fitsarinta da kuma yawunta.(urine ,feaces,saliva)._
_TO MEYE SHAWARA AKAN WANNAN HALITTAR ?_
_Da zaran an ganta akashe ta ayi amfani da takalme ko tsintsiya._
_Kada a ganta a cikin ruwa ko abinci a dauka a sha._
_Bata son tafarnuwa ko kadan,dan haka a rinka jefa tafarnuwa a inda take zata gudu ta bar wajen_
:
```Allah ta'ala yasa mudace```