Matashin da ya daɓawa maƙocinsa wuƙa a maƙogoro saboda murnar zaɓe a KANO ya gurfana gaban kotu

 TSARO

Matashin da ya daɓawa maƙocinsa wuƙa a maƙogoro saboda murnar zaɓe a KANO ya gurfana gaban kotu

Kotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta a unguwar Kwana huɗu Kano , ta yi umarnin tsare wani matashi bisa zargin yin amfani da sharɓeɓiyar wuƙa ya Daɓawa Mahmud Auwal Giginyu a maƙogoransa.

Ana zargin Sa’adu Abdul’aziz da ake yi wa laƙabi da Goje da samar da mummunan rauni ta hanyar Daɓawa Mahmud Auwal Giginyu wuƙa a maƙogoransa , bayan ya buga musu Nok-Out na murnar cin zaɓe.
Matashin da aka jiwa mummunan raunin ya yi masa magana ne , amma sai ya shiga gida ya ɗauko wuƙa ya daɓa masa a Maƙogoro.
Mai gabatar da ƙara Aliyu Abidin Murtala ya karanto masa ƙunshin tuhumar da ake yi masa, inda nan ta ke ya amsa laifinsa.
Mai shari’a Mallam Nura Yusuf Ahmad ya bayar da umarnin tsare shi a gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya har zuwa ranar 28 ga watan April 2023 , dan ganin yanayin raunin mai ƙara yake ciki da kuma yin hukunci a

Post a Comment

Previous Post Next Post