CUTAR AL'AURA TA MATA. (VAGINITIS DISEASE


 CUTAR AL'AURA TA MATA. (VAGINITIS DISEASE)

👇🏾


VAGINITIS : Wata cutace da mafiya yawan jama'a suna kiranta da Vaginal Infection  sabida wannan matsalar tana addabar gaban mace . Amma a Hausance ana kiranta da Ciwon Sanyin Mata.


Wannan cutar wassu kwayoyin cutar Bakteriya da Fungus dake zaune acikin Gaban mace su suke kawoshi.


Ana Iya samun wannan ciwon a lokocin juna biyu (ciki) da shayarwa , haka kuma za'a iya samun ciwon ta hanyar jima'i .


CAUSES OF VAGINITIS:

👇🏾


1- Bacteria Vaginosis : wannan wani kwayar cutace dake rayuwa  cikin farji yakan haddasa matsalar Sanyin mata .


2- Candidiasis : wannan wata kwayar cutace Wanda yake haddasa Sanyin Gaba. Wadannan kwayoyin cutar suna zama cikin farji kuma basu cika cutarwa ba, wadannan kwayoyin cutar suna son waje mai gumi domin su girma dan yaduwa.


3- Trichomonas Vaginalis  : wannan itace wacce take yaduwa ta hanyar jima'i. Ita wannan kwayar cutar parasite ce take kawoshi .


4- Irritation Vaginitis : ita wannan ana kiranta da Allergic , wassu abubuwanda jikin mutun bai daukesu ba, anasamunsa wajen amfanida kamar su condom, sabulu , ko maganin shafawa.


SIGN AND SYMPTOMS


1- Kuburin Farji

2- Canxa Launin Farji zuwa Ja.

3- Kaikayin Farji

4- Warin Farji

5- Kurajen Farji

6- Zubar da Farin ruwa a Farji.

7- Zafin Lokocin Jima'i

8- Zafin Fitsari.


PREVENTION OF VAGINITIS:

👇🏾

1- Avoid Vaginal Douching : A cikin Farji akoi wassu kwayoyin bakteriya wadanda basa cutarwa kuma sunada amfani , amfaninsu shine suna taimakawa wajen bada kariya ga Farji , sai kaga wassu matan sukan wanke Farji da Sabulu ko detol haka , wadannan abubuwanda ake amfani wajen wanke farji yakan kashe bakteriya masu amfani na Farji , Sai masu cutarwa su samu daman shiga.  A kiyaye wanke Farji Da Sabulu dakuma wadansu abubuwa Wanda bamusan Kansu ba.


2- Uses of Underwear : Amfani da wandon pants , wassu matan sukan bar wandonsu yayi datti , Barin datti ko amfani pant masu datti yakan bawa kwayoyin cuta daman shiga Farji.

A Tsaftace wanduna.


3- Cleaning Faeces : wajen wanke bahaya mafi yawa mata sukan dauki kwayar cutar da take dubura zuwa Farji, wanda basa yiwa dubura illa amma sukan yiwa Farji illah.

 Shawara shine afara wanke Farji kafin a wanke dubura.


4- Sharing of Underwear:  amfani da pants na wassu , ta yiu wacce kuke amfani da pants daya tanada cutar Sanyi idan kinyi amfani da nata kema zaki iya dauka.

Sai a kiyaye.


5- Sexual intercourse : mutun yakan iya daukan wannan cutar lokocin saduwa da namiji shawara itace adinga amfanida Condom lokocin saduwa.


Shawara Idan mace taga daya daga cikin wadannan alamomi da muka lissafa daga sama ta garzaya zuwa asibity domin agane me yake damunta kuma abata maganin da ya dace da ita, domin wannan matsalar ba na kemis bane .


Mashkur Abdullahi Tsafe

Health educator

Post a Comment

Previous Post Next Post