Gobarar daji ta mamaye tsaunukan Kenya.

 Gobarar daji ta mamaye tsaunukan Kenya



Kenyan mountain forests

Gobabar daji ta ƙona daji mai girman gaske a yankin tsaunukan Aberdare da ke tsakiyar ƙasar Kenya.

Gobarar wadda aka fara samun rahotonta a dazukan gandun dajin Aberdare makonni biyu da suka gabata, ta ci gaba da yin É“arna duk da É—aruruwan jami’an kashe gobara da aka tura zuwa yankin domin kokarin shawo kan ta.

Gobarar ta kashe jami’an hukumar kula da namun daji ta Kenya guda biyu a lokacin da motarsu ta samu matsala yayin da suka garzaya wurin a rana ta biyu.

Wani mai kula da gandun dajin, Bakari Mungumi, ya shaida wa BBC cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kan musabbabin tashin gobarar.

Tsawon lokaci da aka É—auka ana fuskantar fari a kan tsaunukan, ya janyo bushewar dazuka wanda barazana ce muddin gobara ta tashi.

"Ƙaruwar yanayin zafi da busassun ciyayi, na ƙara tsananta lamarin, don haka yana da wahala a kashe gobarar," in ji mista Mungumi.

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake samun gobara a yankin ba. A cikin shekara ta 2012, gobara ta lalata daji mai girman gaske.

Tsaunin Aberdare, ita ce ta uku mafi tsayi a tsaunukan Kenya, wanda ya kai kusan mita 4,000.

Post a Comment

Previous Post Next Post