HAKKIN MIJI DA MATA AKAN JUNANSU

 

•HAKKIN MIJI DA MATA AKAN JUNANSU•


1• Soyayya ta gaskiya:


Dolene kayiwa matarka soyayya ta gaskiya haka kema dolene agareki,


Domin saida soyayyar gaskiya zaka iya kulawa da dukkan damuwarta, 


Itama saida soyayyar gaskiya zata iya biyayya ga mijinta.


2• Tsare Amana.


Wajibi ne Mace ta tsare amanar mijinta, tundaga jikinta da dukiyarsa dama duk wani sirrinta da nasa ta kula dasu.


Haka kaima wajibine ka tsare mata amanar dukkan gaɓɓanka kada ka nemi mata a waje, banda kallan mata a waje, banda kula mata inba wata larura mai ƙarfi ba.


Kakuma tsare mata sirrinta da duk wani abu daya shafeta.


3• Tausayawa juna.


Wajibine miji yarinƙa tausayawa matarsa, saboda ita mace mai rauni ce, ga ayyukan gida ga girki da sauransu.


Haka kema wajibine ki rinƙa tausayawa mijinki kada ki rinƙa ɗora masa nauye-nauye kizama mai haƙuri da iya abinda ALLAH ya azurtaku dashi.


4• Shige da fice.


Baya halatta mace ta rinƙa fita ba tareda iznin mijinta ba, koda leƙe ta window ko ta ƙofar gida haramun ne ga mace.


Haka kaikuma ka kiyaye dawowa akan lokaci saboda duk mace tanaso mijinta yadawo gida akan lokaci.


5• Kada tayi azumin Nafila saida izninsa, ssboda zai iya zuwa da buÆ™atarsa alhali kuma tana cikin azumi, to anan ana iya samun matsala, kodai a karya azumin kokuma shi yashiga takura.


6• Duk lokacin da mijinki yazo da buÆ™atarsa wajibi ne ki amsa masa, haka kaima wajibi ne idan tazo maka da buÆ™atarta ka amsa mata, domin ita sha'awa wata larurace mai Æ™arfi, saidai idan matar tana cikin halin haila.


6• Wajibi ne mace ta saurari mjinta idan yana magana da ita, kadata rinÆ™a ja'injadashi da gardama.


Haka shima idan tana magana anaso ya nutsu ya saurareta yakuma yi mata magana cikin sanyin murya.


7• Kada mace ta rinÆ™a raina abinda mijinta yabata, haka kuma kada shima ya rinÆ™a raina kyautatawar da take masa.


8• Mace ta rinÆ™a ado da kwalli wa mijinta ta rinÆ™a É—aukar kanta itafa amaryace a kullum tana zuba ado.


kaima ka rinƙa yi mata ado kana ƙamshi ka rinka zama kuma kuna hira acikin adon kace nayi wannan ne sabodake, ku yawaitawa junanku yin hakan, kai ka rinƙa ɗaukar kanka a matsayin ango haka itama.


9• Mace ta rinÆ™a gaggawar bawa mijinta haÆ™uri a duk lokacin data yi masa laifi, shima kada yayi girman kai ya amsa mata,


Haka kuma idan yayi mata laifi shima ya rinƙa bata haƙuri hakan yana kawo soyayya mai ƙarfi da kuma zuri'ah mai kyau.


10• Mace ta zama mai kyakkyawan hali ga mijinta, kaima kazama mai kyawawan hali ga matarka.


11• Miji ya maida matarsa abokiyarsa, itama ta rinÆ™a abota da mijinta su rinÆ™a hirar soyayya akoda yaushe.


12• Miji ya rinÆ™a goyo matarsa idan itama zata iya ta rinÆ™a goya mijinta lokaci-lokaci.


13• A lokacin kwanciyar aure a rinÆ™a gabatar da wasanni wa juna, a Æ™alla ayi wasa da juna kamar na 1hour, yadda sha'awar kowa zata motsa sosai, kuma dukkan jiki ya amsa.


14• Ka rinÆ™a yi mata murmushi a duk lokaci data kalleka, haka kema ki rinÆ™a masa murmushi a duk lokcin daya kalleki.


15• A duk lokacin da akai kwanciyar aure a rinÆ™a nunawa juna farin ciki da nuna jin daÉ—in juna, a kuma rinÆ™a kwanciya a jikin juna, kowa ya rinÆ™a nuna damuwarsa idan É—aya baya jikinsa a yayin bacci.


16• Ki rinÆ™a yiwa mijinki addu'a a duk lokacin da kikai sallah, kina masa fatan alkhairi, 


kaima ka rinƙa yiwa matarka addu'a kana yi mata fatan alkahiri aduk lokacin da kayi sallah.


17• Idan ka fita aiki ko kasuwa ka rinÆ™a kiranta kana jin muryarta kana kuma yi mata godiya da yadda take haÆ™urin zama a gida kana yaba mata.


Kema ki rinƙa kiransa kina gaisheshi kina masa fatan alkhairi, kina kwantar masa da hankali.


18• Idan mijinki yadawo ki tareshi da murna da farin ciki, ki kuma karÉ“i abinda ke hannunsa.


kaima kashigo kana mai murmushi da farin ciki kuma katari matarka kana mai nuna mata farin ciki.


19• Sannan miji ya rinÆ™a neman shawara a gurin matarsa, itama ta rinÆ™a shawara da mijinta akan wasu keÉ“antattun lamura.


20• Sannan ku rinÆ™a taimakawa matanku da Æ´an kuÉ—aÉ—e, wanda yakeda hakli ya saka mata albashi, wanda baida hali kuma yarinÆ™a yi mata kyauta na kuÉ—i lokaci-lokaci saboda tana iya yin baÆ™i waÉ—annan kuÉ—aÉ—e zasu taimaka mata wajen fitar daku kunya kai da ita.


Zan dakata anan insha ALLAH wani lokacin zamu ƙaro wasu ladubba na zamantakewar aure.


ALLAH kabamu ikon aiki da abinda muka karanta.


ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki É—aya.

Ameen...

Post a Comment

Previous Post Next Post