Ko ki san cewa zaki iya samun zuciyar namiji da wasu abubuwa kadan?

 Danna kan photo domin save a wayar ka 👇


Ga masu bu gatan shiga WhatsApp group sin mu ga link 👇

https://chat.whatsapp.com/BjmIOriecuI285DP953VfZ

Ko ki san cewa zaki iya samun zuciyar namiji da wasu abubuwa kadan?


1.LADABI DA BIYAYYA

Zaki samu zuciyar namiji da wannan babban makamin wato ladabi da biyayya,koda zuciyar sa dutse ne muddin kina masa ladabi da biyayya zaki samu kan sa,maza na son ladabi da biyayya hakan na kara masu kaunar mace.


2.HAKURI

Abu ne wanda sai da juriya domin hakuri abu ne sai an jure, musamman zaman tare daman hakuri ya shine gaba.dole ne wani abin sai an yi hakuri wani kuma sai anyi magana.


3.IYA MAGANA

Kyawawan lafazi yana da kyau mace ki iya magana,ba kowane magana bane ake fadawa Namiji.


4.IYA KWALLIYA 

Kwalliya na matukar jan hankalin namiji,ko da mace ke ba kyakkyawa ba ce wannan kwalliyar yana saka ki kiyi kyau, maza na son ganin mata sun iya kwalliya da ado.


5.GIRKI

Babban makamin diya mace kenan,duk kyan ki da wayewar ki,idan baki iya girki ba kawata akwai matsala,koyan girki tun kina gida ake yi,da wannan iya girkin shima tsaf zaki samu zuciyar namiji.


6.SON IYAYEN SA DA DANGIN SA

Bafa namiji mai hankali da zai yarda ki wulakanta masa iyaye ko 'yan uwan sa,duk kowa son da yake miki bazai yarda ba muddin yasan hankali sa ya kuma san mutuncin iyayen sa.

wannan bangaren ma mata idan kuka gane zaku sami zuciyar namiji.


7. SOYAYYAH

Maza na son macen data iya soyayyah kuma take nuna masu,da soyayyah ana samun zuciyar namiji domin lokaci kadan sai namiji ya fada son ki.


©️ Nusaiba Tasiu Abdulrahim

Post a Comment

Previous Post Next Post