MIYAR AYAYO DA KUBEWA
Kayan hadi
ayayo kubewa maggi manja ko mangya daddawa attaruhu albasa kifi ko nama citta kanunfari
METHOD
Ki samu kubewarki me kyau ki wanketa tas kiyanka,saiki wanke ayayonki shima ki tsinkeshi saiki yankashi shima ki aje gefe.
Saiki dora tukunyar miyarki a wuta idan nama zakiyi amfani dashi saiki tafasa shi da spices saiki sauke,inkuma kifi ne saiki wanke ki Gyara ki aje.
Saiki sa tukunya kizuba manja ko mangyada kizuba Yar albasarki idan namane saiki zuba kisoyashi sama sama saiki zuba kayan miyarki saiki sa daddawa citta da kanunfari saiki zuba ruwan tafashenki ki kara ruwa kitsaida ruwan miya.
Inkuma kifine to bayan kinsa k/miya saiki zuba komai amma banda maggi saiki sa kifi kirufe
Kibarshi ya dahu.
Saiki kiba ayayonki idan miyar tayi kinga ruwan yakone saiki fara zuba ayayonki zuwa minti 4-5 saiki zuba kubewarki kibarshi ya dan Baraka saiki dau tsintsiyar miyarki kikara burgeshi zaki iyasa kanwa Yar kadan saiki sauke ki zuba maggi yanda kikeson dandanonki.