SIRRIN WARWARE SIHIRI DA RABUWA DA #JINN_ASHIQ DA YADDAR ALLAH..

 


SIRRIN WARWARE SIHIRI DA RABUWA DA #JINN_ASHIQ DA YADDAR ALLAH..


Assalamu Alaikum


Da fatan kowa yana lafiya..?

ALLAH ya bar zumunci ameen.


Wanda akayiwa sihiri ko yake fama da matsalar aljanu ko macen da aljanu suka dameta, suka hanata aure ko dan kasuwar da aka jefi kasuwar sa ko da an hada da jinnu ne a sihirin da aka masa INSHA ALLAHU aka jarraba wannan sirrin za ayiwa ALLAH godiya mu kuma za ayi mana addu'ar fatan alkhairi INSHA ALLAHU domin za a rabu da wannan matsalar BI'IZINILLAHI TA'ALA.


GA YADDA AKE YIN WANNAN SIRRIN MAI ALBARKA KAMAR HAKA.


Ana farawa kowacce rana kuma kowanne lokaci. Ana dauro alwala sai a samo #TAFARNUWA guda 41 sai a samu waje marar hayaniya sai a samo garwashin wuta sai a kalli alkibla..


Sai a dauki silin tafarnuwa guda 1 a karanta #Ayatul_Kursiyyu kafa 1 a tofa a jiki sai a saka tafarnuwar a cikin wutar sai a tari hayakin a bude baki da hanci da idanu hayakin ya shiga sosai.


Sai a kara daukar tafarnuwa ta 2 itama ayi mata yadda akayi da farko dai haka sai an gama da guda 41 din...


Kullum ayi haka kwana uku a jere dai IZININ ALLAH aka daure akayi wannan sirrin Za a samu waraka INSHA ALLAHU.


Idan mutum bazai iyayi da kansa ba zai iya sawa wani yana karanta masa shi kuma sai yayi daga baya.


INSHA ALLAHU macen da aljanu suka dameta idan tayi wannan sirrin zata samu waraka. Wanda kuma ya daure yayi koda babu komai a tare dai shi to ya yiwa kansa raga-kafi INSHA ALLAHU.


Al'amuran kasuwanci zasu dawo dai dai.

Post a Comment

Previous Post Next Post