Nau-ukan abincin da ya dace a fara bawa jarirai...daga lokacin da suka fara cin abinci da ruwa wato wata 6 zuwa shekara biyu

 


Nau-ukan abincin da ya dace a fara bawa jarirai...daga lokacin da suka fara cin abinci da ruwa wato wata 6 zuwa shekara biyu


Ba ko wane abinc ake bawa jariri ba idan ya fara cin abinci a'a ana bin matakai ne daga kasa sannan ai sama..ga yadda ya dace ayi dan in ganta lafiyar jarirai


Watanni 6 zuwa 8: A fara da abincin da aka dama kamar kamu, cerelac, kunun gyada da sauransu.

Za a iya ci gaba da ba da abinci mai ruwa-ruwa kamar faten dankali sau 2 zuwa 3 a rana, gami da shayarwa, dangane da bukatar jaririnki.

A fara da karamin cokali biyu zuwa uku daga farko-farko. Sa’annan daga bisani a iya karawa.

Watanni 9 zuwa 11: Bayan irin mai ruwa-ruwa na sama, fara ba da sauran abinci mai kauri amma wanda aka mutsuke kamar kwai, naman kaza mai laushi da sauransu. A fara da kayan marmari ba ruwan juice ba sau 3 zuwa 4 a rana gami da shayarwa dangane da bukatar jariri. Rabin karamin kofi.

Watanni 12 zuwa 23: A wadannan watanni kusan za su iya cin duk wani abinci mai laushi ko da ba a mutsuka ba. Sau 3 zuwa 4 a rana gami da shayarwa daidai da bukatar jariri.

   

Mashkur Abdullahi Alkali Tsafe

Health Educators


Post a Comment

Previous Post Next Post