HAIHUWA A LIKITANCE

 


HAIHUWA A LIKITANCE


A lissafin masana kiwon lafiya ana kyautata zaton mace mai ciki za ta haihu ne tsakanin makonni 38 zuwa 42.


Da zaran mace tashiga makonnin nan zatafara jin wadannan alamomin (alamomin nakuda)

- Yawan fitsari

- Daurewar mara

- Ciwon mara

- Ciwon baya

- Nauyin Ciki

- fitar da wani Abu mai kamar majina a bakin mahaifa.


A duk lokocin da kika fara samun wadannan alamomi kije asibity kiyi  magana da ingozuman ki akan na’kuda da kuma hanyoyin da zakibi ki haihu lami lafiya, da kuma me yakamata ki tanada kafin lokacin haihuwar tazo.


Sabida haihuwar gida nada hatsari sosai musamman ga wadannan mata :


1- Mace mai ciki na farko

2- Mace mai ciki na shidda zuwa gaba.

3- Idan kwanciyar yaro baiyi daidai ba.

4- Wacce take samun alamun kunburin kafa.

5- Idan ana tsammanin tagwaye ne.

6- Idan mace ta taba samun zubar jini bayan haihu.

7- Idan mace antaba yi mata tiyata na haihuwa.

8-  Macen da batada tsawo (gajeriya)

9- Mace mai rashin jini.

10- Matar da take samun zubar jini.


Sabida haka muna kira ga dukkanin mata kada suyi gangacin haihuwa a gida domin tana da hatsari sosai.


IDAN AKA SAMU AKASI AKA HAIHU A GIDA:


Ko an ansamu akasi aka haifi yaro a gida dole za'a dauko yaro zuwa asibiti, amma kafin azo asibity abin da ya kamata ayi sune:


1- Da zaran an haifi yaro adan jinkir ta kafin a yanke mabiya da sabon razer a kalla minti daya zuwa biyu.


2- Ayi kokorin share majinar dake bakin yaro da auduga mai tsafta.


Yin hakan gaskiya zai taaimaka wajen ceton rayuwar jarirai.


3- Lokocin da aka haifi yaro a kifar da shi a kirjin mamar sa ( skin to skin contact).


4- Kada ayiwa jariri wanka, a daukeshi a yadda yake zuwa asibiti koda lafiyar sa kalaw ne.


5- A taimaka a saka jariri a nono tun kafin aje asibity, da zaran a goge majinar bakin sa a tura shi a nono.


6- Kada a saka komai a cibiyar yaro da sunan magani sai anje asibity.


Allah ya saukar da masu juna biyu lafiya Amin


Mashkur Abdullahi Tsafe

Health educator

Post a Comment

Previous Post Next Post