Turkashi: wani matashi ya halaka mahifin sa lahira sabida ya tashe shi daga bacci.

 

Turkashi: wani matashi ya halaka mahifin sa lahira sabida ya tashe shi daga bacci.

Hukumar ‘yan sandan jihar Ogun ta bayyana cewa ta cafke wani matashi mai suna Ibrahim Sikiru, mai shekaru 27, bisa zargin halaka mahaifin sa da adda a yankin Onipanu a cikin jihar. Jaridar Pulse.ng ta rahoto.

Kakakin hukumar, DSP Abimbola Oyeyemi, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa ga manema labarai a Ota, inda ya bayyana cewa an cafke wanda ake zargin ne a ranar 30 ga watan Maris.

Oyeyemi yayi bayanin cewa an cafke matashin da ake zargin ne bayan wani mai suna Abiodun Sunday, ya shigar da Æ™orafi a ofishin hukumar ‘yan sanda na Onipanu.

Post a Comment

Previous Post Next Post