YADDA ZAKI KULA DA GABANKI


 YADDA ZAKI KULA DA GABANKI


Kamar yadda muka kawo Hanyoyin da maza zasu kula da lafiyan azzakarinsu wannan makon kuma mu zo da Hanyoyin da mata zasu kula da farjinsu. Saboda abubuwan biyu guda daya ne. Idan mara lafiya ya shiga mai lafiya dole ne shi ma rashin lafiyan ya shafe shi. Don haka samun illimin kula da su biyu yana da amfani.
Mata sun fi maza hadarin kamuwa da cuttutuka masu halaka da shiga cikin farjin su. Shi yasa a kullum suke yawan zuwa ganin likita domin neman lafiya.

Akwai matan da suke kokarin kula da tsaftace gabansu amma a rashin sanin hanyoyin dasu ke bi yana da illa matuka.
Ga wasu hanyoyi masu sauki yadda mata zasu iya kula da lafiyar gabansu.

1: Ga mata masu aure kuma masu son a musu sakace. Kada mijinki ya rika tura miki yatsa ba tare da kin tabbatar da ya tsaftace hannunsa da kuma faratansa ba. Saboda kananan cuttutuka masu shiga jikin mutu suna iya makalewa a farata.

2: Kada ki rika saka wandon pant da yake jike. Wannan danshin yana iya zama miki a jiki ya cutar da gabanki.

3: Kada ki rika kwara ruwa a gabanki dayawa. Misali ki bude shower kai tsaye ruwan yana fesowa a gabanki wannan yakan jawo cuta a gaban mace.

4: Shi gaban mace yana da ruwa na musamman dake wanke shi. Don haka idan kika ga ruwa na yawn fita a gabanki muddin ba mai wari ko doyi bane kaga kice zaki rika sa tissue kina katsewa, wannan ruwa na lafiyan gabanki ne sai dai kina iya samun ruwa mai dumi kin tsaface gaban ki dashi.

5: Ki guji fesa turare ko foda a gabanki. Wadannan suna da sinadarin dake iya cutar miki da gabanki.


Post a Comment

Previous Post Next Post