Kungiyar tsaro ta Nato ta yi Allah-wadai d mtakin da Rasha na kafa wata tashar makamin nukilya a Belarus.
Kungiyar na bibiyar lamuran da suke faruwa sau da ƙafa, kuma matakin Rashan ba zai sa ta sauya manufofinta ba kan makaman nukiliya.
Amurka ta ce ita ba ta yarda ba, kawai Rasha na son amfani da makaman ne.
Belarus ta yi iyaka da Ukraine da kuma wasu ƙasashe da ke ƙungiyar Nato da suka haɗa da Poland da Lithuania da kuma Latvia.
Tuni Ukraine ta yi kiran wata tattaunawar gaggawa da kwamitin sulhu na Majalisar ÆŠinkin Duniya kan wannan sabuwar barazana da shugaba Putin ya sanar a ranar Asabar