Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta bayyana cewar, har yanzu dokar nan ta haramta zirga-zirgar baburan adai-daita sahu, a jihar, daga ƙarfe 10 na dare, zuwa 6 na safe, na nan daram, inda ta buƙaci matuƙa baburan da su cigaba da kasancewa masu biyayya ga dokar.
Ka zalika, rundunar ta kuma sake bayyana haramcin yin kilisa da Dawakai, a ƙwaryar birnin jihar, musamman a wannan wata mai Alfarma, na Ramadan, da mu ke ciki.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, shi ne ya bayyana hakan, ga manema labarai, a birnin Kano