An jefe Direban Adaidaita Sahu har lahira bayan da ya cakawa fasinja wuƙa a ciki

 

An jefe Direban Adaidaita Sahu har lahira bayan da ya cakawa fasinja wuƙa a ciki.

 

Wasu fusatattun matasa sun jefe wani direban babur ɗin adaidaita sahu sakamakon zargin sa da kashe wani fasinja.

 

Wannan lamari dai ya faru ne a garin Yenagoa dake jihar Bayelsa.

 

A ranar Laraba da ta gabata ne, rahotanni su ka ce, lamarin ya faru, bayan da direban adaidaita sahun ya cakawa wani fasinja da ya ɗauko wuƙa wanda sanadiyar haka fasinjar ya rasa ransa nan take, wannan shi ya janyo wasu matasa dake kusa da inda abin ya faru suka jefe direbar adaidaita sahun da duwatsu har sai da ya mutu.

 

Shaidun gani da ido sun ce tun farko direbar adaidaita sahun sun samu matsala da fasinjar da ya ɗauko ne kan canji Naira hamsin wanda sanadiyar haka ne direbar adaidaita sahun ya fusata ya ɗauki wuƙa ya caka masa.

 

Rundunar yan jihar Bayelsa ta tabbatar da faruwar lamarin

Post a Comment

Previous Post Next Post