Anci Gaba Da Gwabza fada Yanzu Haka a Babban Birni Kartoum Dake Kasar Sudan


 Anci Gaba Da Gwabza fada Yanzu Haka a Babban Birni Kartoum Dake Kasar Sudan. 


Daga Real Alameen Minister Yakasai


Banda tashin manyan bindigogi da jiregen yaki babu abin da ake iyaji kawo yanzu dai har ma da wasu yankunan na kasar Inda mutane da dama suke ta kokarin ganin sun tsira da ransu amma abin yaci tura sakamakon babu hanyar fita.


Saidai babban tashin hankalin da dalibai yan asalin Nageria suke ciki yanzu abin tausayi ne dama sauran mutanan da harkar kasuwancin ne yakai su wannan yakin ya ritsa dasu.


Naga faifai bidiyon wata daliba yar Nageria tana Kuka tana Sanarwa da duniya irin halin da suke ciki harma acikin take bayanin cewa idan har suka mutu a wannan kasar ta sudan bazasu Taba Yafewa Gwamnatin Nageria ba.


Abin tambayar anan wanne irin kokari gwamnatin Nageria takeyi akan wannan lamarin  duk da kiraye kirayen da mutanan kasar sukeyi na gani gwamnati tayi abin daya kamata kafin lokaci ta kuremata.


Wannan yakin dai kullum kara tsananta takeyi gashi babu ruwan sha babu wutar lantarki uwa uba kuma babu abinci yanzu hakan babu kuma wata hanya  da zasu iya samun Wani taimako gaggawa.


A Wani bangaran ma ana maganar cewa  anfasa gidajen yarin dake wasu yankunan Inda wayanan daurarrun suka soma zaman barazana ga wayannan daliba yan makaranta.


Koma dai menene yakamata gwamnati ta Kalli wannan lamarin da idan basira tunkafin azo ana da ansanin da  bazayiwa kowa amfani ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post