ABUBWAN DAYA KAMATA MUTANE SU SANI DANGANE DA CIWON BASIR


Danna link domin shiga WhatsApp group dinmu👇👇

https://nisauljannaty.blogspot.com/2023/02/yadda-za-wanke-qoda-kidney-cikin-sauki.html



 ABUBWAN DAYA KAMATA MUTANE SU SANI DANGANE DA CIWON BASIR
utar ciwon basir ciwo ne da ke haddasa kumburi da radadi mai tsanani a duburar mutum (lowest part of rectum and the anus). Ciwon kan ko haddasa rashin jin dadi a wurin da kuma zubar da jini wani lokacin. Ciwon basir ya kasu kashi biyu ne; a kwai na waje (edternal hemorrhoid) da kuma na Ciki (internal hemorrhoid). Ga bayanansu kamar haka:


Ciwon basir na Ciki dubura (internal hemorrhoid):


Kamar yadda ake kiran shi, wannan ciwon Basir na daga cikin duburar mutum (inside rectum) ne. Mutum ba ya iya taba shi da hannun saboda ya na boye ne ta Ciki. Yawanci irin wannan Basir din bai da zafi, saboda a wurin da ya ke, wato rectum. Abinda ke sa mutum ya ji zafi kadan ne, wato yana da pain-sensing nerbes dan kadan. A kan gane mutum na fama da irin wannan Basir ne in ya na zubar da jini, wato yana bleeding, a Turance.


Ciwon Basir na wajen dubura (edternal hemorrhoid):


Ciwon Basir na wajen dubura dai shine wanda yake fitowa a kan fata ta wajen dubura (anus). Shi wannan irin ciwon Basir ya na da zafi ko kuma ace yana da radain gaske saboda wurin na da abinda ke haddasa radadin cikin sauri. (pain-sensing nerbes). Wani dan kumburi kan samu a wurin wanda kan kunshi jini (blood clot), bayannan wannan kumburin sau da yawa, nau’in shi kore ne, wato blue ko kuma purple. Ya kan haddasa zafi mai tsanani da kaikayi harma ya kan yi jini wani lokacin. Ko da kumburin ya sabe wato ya warke mutum kan dade da shi kadan, abinda kuma ke haddasa wani dan rashin jin dadi a wurin wani lokaci.


Wadanne Abubuwa Ne Ke Sanadiyar Kamuwa Da Ciwon Basir?:


Masana sun yi ittifakin cewar abubuwan dake jawo ciwon basir sun hada da:


1. Gado (genetics)


Mutane kan kamu da ciwon Basir ne wani lokaci saboda gado da sukan yi a wajen iyayensu ko kuma danginsu.


2. Kiba (obesity)


Saboda nama da masu kiba kan hada a kasan su (lower rectum), tafiyar jinin su, wato blood flow, kan samu matsala. Hakan ne sai ya sa jijiyoyin wurin su kumbura wanda kuma hakan kan zama ciwon Basir.


3. Juna Biyu (pregnancy)


Mata da yawa kan samu ciwon Basir a yayin da suke da ciki, musamman lokacin da mace ta kai irin wata bakwai ko kuma sama da haka. Wannan Basir ana kamuwa da shine saboda da irin yadda wasu matan kan fuskanci wuya lokacin da suke yin bahaya, abinda ake kira constipation a Turance, dalilin irin matsuwa (strain) da wurin ke samu a dalilin nauyi da suka kara ko makamancin hakan. Wani lokaci kuma nauyin yaro ne kan yi wa uwa yawa sai ya sa jijiyoyin ta na kasa su matsu, to shima wannan yanayi kan haifar da ciwon Basir ga mace mai Juna Biyu.


4. Straining (wato matsuwa)


Matsuwa ba dole sai mace na da Juna Biyu ba ya ke faruwa. Ya kan faru ne saboda wasu dalilai daban. Idan kuma hakan ya faru, ya kan jawo ciwon Basir saboda matsuwa da jijiyoyin kasan mutum (rectum) kan yi, kuma ya kan haifar da kumburi ko kara fadin wurin. A wani lokacin kuma ciwon kan fito waje ya dan yi kumburi haka mai dan laushi bayan nan kuma ya rika zafi a yayin bahaya. Amma yawanci wannan kumburin kan koma don kansa ko kuma in mutum na iya mai da shi a hankali da kan shi.


5. Gudawa mai tsawo ko kuma zawo


Ciwon Basir na faruwa ne idan mutum ya na gudawa mai tsawo, wato ya kasance mutum ya dauki lokaci mai tsawo yana bahaya kuma gudawa. Har’ila yau ya kan abin yana faruwa nea sanadiyar irin bahayar nan dake fita da kyar, wato constipation. In mutum na tari abun kan kara tsananta matuka gaya.


Baya ga wadannan dalilai da aka yi bayani, har yanzu mutum na iya kamuwa da ciwon basir ta:


Hanyar daga kaya mai nauyi


Yawan tsayuwa mai tsayi ko kuma zama mai tsayi.


Tsufa


Abubuwan Da Mutum Zai Yi Don Gujewa Kamuwa Da Ciwon Basir:


Mutum kan iya rage hadarin kamuwa da Basir ta hanyar kula da yadda ya ke tafiyar da rayuwar shi ta yadda ba zai samu matsalar bahaya mai karfi ba, wato constipation. Kuma mutum zai iya cimma sauki ta hanyoyi kamar haka:


Yawan shan abu mai ruwa-ruwa a kalla mutum ya kasance yana shan ruwa kamar kofi 8 zuwa 10 a ko wacce rana. Bayannan ya samu a kalla lemun ‘ya’yan itace (fruit juice) kamar kofi biyu kullun.


Cin abinci mai high fiber: Abinci kamar su danyun ‘ya’yan itace, ganyayyaki (begetables), irin su bran cereal da sauran abinci wanda ya kunshi fiber a ciki.


Yawan motsa jiki: motsa jiki kamar irin walk da aerobics din nan su na da kyau ga lafiya. Amma ya na da kyau mutum ya nemi shawarar kwararru kafin ya fara yin motsa jiki.


Yana da matukar muhimmanci mutum ya kasance ya na zagawa akai-akai (bowel mobement) da ya ji bukatan hakan saboda jinkirtawa kan haifar da constipation.


A kiyaye hada kiba: Mutum ya kamata ya yi kokarin tsayawa a daidai nauyinsa kamar dai yadda kwararru suka tabbatar masa. Hada kiba ya yi yawa kan sa wa jiki nauyi wanda kuma hakan na haddasa ciwon Basir. Yana da kyau a rika yin gwajin nauyi lokaci zuwa lokaci don gudun wuce gona da iri.


A rage yawan tsayuwa ko zama mai tsawo: In har mutum ya kasance sai ya zauna zama mai tsawo soboda sana’arsa ko ko kuma sauran abubuwan da suka kasance dole ne. Wannan ya na da kyau ya rika tashi duk bayan awa daya yana yin hakan haka, ya dan gewaya kadan.


Maganin Ciwon Basir:


Abin murna anan shine yawancin lokaci ciwon Basir na warkewa da kansa. Amma ga wasu hanyoyi da mutum zai bi a samu sauki daga radadin ko kunburin ko kuma kaikayin ciwon Basir:


Zama cikin ruwan dumi (ba ruwa mai zafi ba) na kamar minti 20. A yi haka sau biyu a ko wacce rana.


Idan an tabbatar da basir din yayi yawa sai a gaggauta zuwa Assibiti domin samun ingantaccen magani


Allah yabamu lafiya


Mashkur Abdullahi Tsafe

Health educator

Post a Comment

Previous Post Next Post