CIWON HANTA 'B' (HEPATITIS B) ;


 CIWON HANTA 'B' (HEPATITIS B) ;

Domin shiga WhatsApp group dinai suna kiwon lafiya a musulunci danna 👇 danna



Ciwon hanta ' B '  cutace mai matuqar hadari ga hanta. Cutace datazama barazana ga duniya baki daya, tareda haddasa yawan mace - mace.


A shekarar 2015, Kimanin mutum miliyan 257 ne afadin duniya suke dauke da cutar. 

Sannan Kimanin mutum dubu 887 ne suka mutu sanadiyyar cutar.


ABINDA YAKE HADDASA CIWON HANTA 'B'  ;


Itace Kwayar cutar "Hepatitis B Virus (HBV).


WASU DAGA HANYOYIN DA AKE IYA KAMUWA DA CIWON HANTA 'B' ;


1. Ta Saduwa; 


yayinda ruwan sperm, ko semen, yawun bakin mai cutar suka shiga jikin mutum.


2. Ta hanyar amfani da kan alluran ko reza ko tsinken kitso, ko burushin wanke baki da jininmai cutar yataba. 


3. Ta hazarin ai'ki asibiti musamman masu gwajin jini ko gurin allurar data soki mai cutar ta chakeku.


4. Uwa Zuwa Jariri; gun haihuwa uwa zata iya sawa jaririnta (Perinatal transmission).


HANYOYIN DA BA'A KAMUWA ;


1. Ta hanyar tari

2. Ta atishawa

3. Ta gaisawa


RABE RABEN CIWON HANTA TA FISKAR KAMUNTA ;


1. Qaramin mataki (Acute Hepatitis B) ; 


Shi yake warkewa qasa da wata shida idan garkuwar jiki (immune system) sun kawar dashi.


2. Babban mataki (Chronic hepatitis B) ;


Shine yake dadewa samada wata shida ko har mutuwa, kuma shiyake haddasa cutar qoda, kasawar hanta, jejin hanta dazai iya bayuwa ga mutuwa.


WASU DAGA ALAMOMIN CUTAR HANTA B ;


1. Tsanwar fata da tsanwayen idanu


2. Fitsari mai duhu


3. Tsananin kasala


4. Tashin zuciya


5. A mai


6. Ciwon Ciki


7. Ciwon gabobin jiki.


WASU DAGA MUTANEN DA SUKAFI HADARIN KAMUWA DA CIWON HANTA ;


1. Mutanen da suke yawan buqatar qarin jini akai akai


2. Malaman asibiti musamman masu gwaje gwaje.


3. ' yan gidan yari


4. Masu saduwa barkatai


5. Jarirai yayin aihuwa.


ILLOLIN DA CIWON HANTA 'B'  YAKE JAWOWA A JIKI ;


Idan ba atareshi dawuriba (qaramin mataki "Acute") to zai kai babban mataki (Chronic )

 kuma zai haddasa :


1. Kasawar hanta (liver failure)


2. Jejin hanta ( liver cancer)


3. Ciwon qoda


4. Damejin hanta


WASU DAGA HANYOYIN KARIYA DA GA CUTAR HANTA 'B'  GA WANDA BAI KAMUBA ;


1. Ayiwa yara rigakafin hanta dazarar anhaifesu.


2. Ma aikatan asibiti da 'yan qasa da shekara 18 sutabbatar sunsamu rigakafi idan basuyi abayaba.


3. Ma aikatan asibiti sunrinqa amfani da safar hannu yayin aiki don rage hadarin kamuwa.


4. A kiyaye Saduwa barkatai


5. Akiyaye amfani da reza, ko burushin wanke baki, ko almaqashin yanke qumbar da mai cutar yayi amfani dashi


6. Akiyaye misayar yawu, ko cingom da abokai.


7. Matsa jini akai akai 🚴🏻‍♀🏃🏼‍♂🏋🏼‍♂


8. Abinci mai daukeda sinadarai🍌🍉🍍🥕🍛


Source ;- WHO- Myo clinic


         ALLAH YA TSAREMU BAKI DAYA


Mashkur Abdullahi Tsafe

Health educator

Post a Comment

Previous Post Next Post