DODON matsafa ya shiga Masallaci ya zane Liman ana tsaka da sallar ASUBAHI
Wasu gungun matsafa masu bin addinin gargajiya sun shiga wani masallaci sun raunata limami da wasu daga cikin mamu ana tsaka da sallar asubahi…
Wannan dai ya faru ne a garin Ile-IFE dake jihar Osun a jiya juma’a.
Rahotanni sun ce matsafa mabiya addinin gargajiya na ORO sune suka shiga cikin masallacin lokacin da al’ummar musulmi ke tsaka da yin sallar asubahi, inda suka fara ta kan liman kafin su koma kan mamu.
