KIRISTOCI a UGANDA sun tsere zuwa ETHIOPIA saboda PASTO ya ce za ayi tashin kiyama kwanan nan
Dubban Kiristoci mabiya Cocin Chris Disciples Church (CDC), sun tsere daga ƙasar zuwa ƙasar Habasha domin tsira daga tashin alkiyama.
Mabiya COCIN dai sun yi imanin cewa za a fara tashin kiyama ne daga yanƙin su kuma ƙasa ɗaya ce a duniya za ta tsira ita ce ƙasar Ethiopia saboda haka suka tsere zuwa ƙasar domin tsira
Hukumomi a biranen Kampala da Adis Ababa sun tabbatar da faruwar lamarin, sai dai har yanzu ba akai ga tantance adadin yawan mutanen da suka tsere ba
Shugabannin COCIN Chris Disciples Church (CDC) dai sun shaidawa magoya bayan su cewa kwanan nan za ayi tashin kiyama kuma daga ƙasar UGANDA duniya za ta fara karewa inda kasar Habasha ne kawai za ta rage a duniya.
