Iyayen yara mata ku gane

   Danna link domin shiga WhatsApp group dinmu👇👇

https://nisauljannaty.blogspot.com/2023/02/yadda-za-wanke-qoda-kidney-cikin-sauki.html


Iyayen yara mata ku gane 


Yadda kuke kai yaran ku gidan mazajen su yana daya daga cikin matsalolin da yanzu ake samu a gidajen aure. 


1. Miji ya hada kayan aure/lefe iya qarfin sa ya kai, da kuka tashi saya mata kayan iyaye sai kuka saya mata kayan da sukafi na mijin tsada da yawa.


2. Ya ququta ya kama ko ya gina gida  dai dai qarfin sa, kun je kunga gida kunce kayan da kuka ma 'yar ku yafi qarfin wannan gidan, ko ya chanza ko ku kama masa wani, akayi daya daga cikin hakan. 


3. Kun tashi kai kayan jere, duk kun cika dakuna da falo da kayan 'yar ku kun hana shi ko daki daya da da ake barma miji ya sa yi kayan dakin sa ya sa shima. 


4. Kun tashi kawo kayan gara, kun cika store da kayan abinci makil da zai iya kaisu shekara 1-2 miji bai sayi komi ba. 


5. Kun cika fridge da miya, naman sa, kaji wasu harda kifi da kayan miya ku duk wai a sunan kun ma 'yar ku gata. 


6. Wasu kun kawota da motar da mijin baya hawa. 


7. Tayi auren kune kudin makarantan ta, kune nema mata ko sama mata aiki, kune daukanta fita wani qasar, kune bata kudin up-keep a gidan miji duk da sunan gata 


8. In tayi ciki kune kun kai kun dauko, kune asibiti, kune jego, kune suna, kune... kune... 


Tayaya 'yar ku zata ta6a ganin girma da darajar mijinta alhali duk kofar da zai nuna bajintansa da qarfin sa kun toshe ? 


Tayaya zata ta6a ganin ya burgeta alhali duk kun mata komi ? 


Wani abu zaiyi mata da baku yimata ba da zai sa taga girma ko value din koqarin sa ? 


Tayaya bazata rena shiba ?

Tayaya bazatana masa gadara ba ? alhali ku kuke mata komi


Da an taba ku kuce baya mata komi sai abunda kuka mata, tun da ya aureta ku kuke riqe masa da gidan, matsalar ai tun farko ku kuka rufe kofofin yayi mata dawainiya tunda kun masa komi kun kawo masa komi, wani azama yake dashi da zai dage yayi ko ya kawo dan ya burgeta alhali komi na nan ko an mata shi ? 


Mu gayama kan mu gaskiya abubuwan da a ke ma yara mata yanzu ko a kaisu ko a bi su dashi gidan miji ba yadda za'ayi mata suna girmama mazajen su, gida nashi ko watakil naku, kayan gida duka naku, kayan sawa naku, abincin cin su naku, mota naku........naku... haba 


Shin Kuna ga akwai qofar zaman lafiya a wannan auren ? 


Shi namiji a duk inda aka hana shi ko aka toshe masa yin wadannan dawainiyar automatic an hana shi girma ne, yin wadannan dawainiyar ke sa yaga muhimmancin sa a gida da rayuwar iyali, namiji yakan mutunta abunda yake wahala ake gode masa akai ne.  


Shiyasa a irin wannan auren ko tari mace ko iyayenta su kayi zaice an renashi ne, shiyasa ku kunaga kamar kun masa gatane dan su zauna lafiya amma duk da haka zama ba dadi, gaskiya zama bazai taba dadi ba a irin wannan auren, don kunma auren qullin minti.


Ya kamata ku iyaye ku rage yin wasu abubuwan, ku barma miji kofofin da zai nuna bajintan sa a matsayin sa na maigida kuma jagora. 


✍️

Post a Comment

Previous Post Next Post