Tunatarwa ga mata


 Tunatarwa!


1. A wanke Baki kafin a kwanta bacci Tooth brush/ chewing stick)


2. A riƙa wanke harshe yayin goge Haƙora ( Tooth brushing/ chewing stick).


Da yawanmu muna goge Haƙora ne kaɗai mu kurkure Baki muyi gaba wanda kuma goge harshen yana taka muhimmiyar rawa wajen kare samuwar cututtuka a Baki.

Sannan wanke harshe ya taimakawa wajen samar da cikekken É—anÉ—anon Abin ci/ sha.


Wani zaiyi ta maka complain na baya jin ɗanɗano mai kyau, idan ka duba harshen sa kaga kamar ka saka wuƙa ka kankaro datti 😥.


Idan baka wanke harshe to ka fara yau kuma yanzu zaka ji sanji sosai inshaa Allah.


Idan baka taɓa wankewa ba, kana tunanin baya Datti, to ka duba madubi kafin ka wanke,sai ka sake dubawa bayan ka wanke, zaka tabbatar da yana Datti.


Allah yasa mu dace.


© Ibrahim Usman

27th Rajab, 1444AH / 18th February, 2023


#IbrahimUsman #DentalTherapist  #oralhealthawareness

Post a Comment

Previous Post Next Post