An cire Naja'atu Muhammad daga aikin sanya ido kan 'yan sanda lokacin zaɓe

 An cire Naja'atu Muhammad daga aikin sanya ido kan 'yan sanda lokacin zaɓe


Hajiya Naja'atu

A wata sanarwa da hukumar ta fitar ta ce an janyo hankalinta ne kan wata sanarwa da jam'iyyar APC mai mulki ta fitar, inda ta yi zargin cewa Hajiya Naja'atu na goyon bayan wata jam'iyya don haka APCn take gani ba za ta yi wa jam'iyyar adalci ba.

A sanarwar da APCn ta fitar mai ɗauke da sa-hannun daraktan yaɗa labaran yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Jam'iyyar Festus Keyamo ya yi watsi da naɗin Hajiya Naja'atu a matsayin mai lura da ayyukan 'yan sanda a lokutan zaɓen ƙasar.

Sanarwar da hukumar 'yan sandan ta fitar ta ce ta maye gurbinta da tsohon mataimakin babban sifeton 'yan sandan ƙasar Bawa Lawan domin lura da ayyukan 'yan sanda a shiyyar ta arewa maso yamma.

Hukumar ta ce a kodayaushe tana taka-tsan-tsan a ayyukanta kuma za ta ci gaba da taimakawa wajen tabbatar da wanzuwar da dimokradiyya a ƙasar.

Haka kuma ta sake jaddada ƙudurinta na tabbatar da samun sahihin zaɓe a ƙasar

Post a Comment

Previous Post Next Post