Yanzu-Yanzu: An Kama ‘Yan Daudu Masu Lalata da Mata 78 A Kano

 

Yanzu-Yanzu: An Kama 'Yan Daudu Masu Lalata da Mata 78 A Kano

Yanzu-Yanzu: An Kama ‘Yan Daudu Masu Lalata da Mata 78 A Kano 

Yanzu-Yanzu: Babbar Hukumar Hisbah dake jihar Kano tayi nasarar kama wasu matasa kwaya 78 a cikin jihar tamu ta kano daya kunshi mata da maza bisa zarginsu da ake na lalata da juna da kuma sanya tufafin da basu dace ba.

Gwamnatin jahar kano tana kokari wajan yaki da haramta dukkan wasu ayyukan fasikanci a karkashin jagorancin Shari’ar Musulunci da ke cikin garin.

Shugaban nata wato Haruna Ibn Sina, shine Kwamandan Hukumar Hisbah ta cikin Jihar Kano, ya ce an kama su ne a wata cibiyar taro da ake kiran ta da suna(White House)da ke cikin Unguwar Nasarawa G.R.A anan Kano.

Shugaban Hisbah ta jihar kano ya ce wadanda ake zargi da laifin sun musanta zargin da ake musu na daurin auren jinsi daya.inda ya ce suna murnane kawai na zagayowar ranar haihuwar takwarar sune kawai.

Amma a Lokacin da rahoto yazo munyi sauri mun garzaya waje da abin ya faru.Amma kuma da isar mu wajan bamu iya tabbatar da cewa suna auren jinsi daya ba ne kamar yadda labari yazo mana.Amma dai mun kama su a cikin wani irin yanayi na rashin da’a tare da mata da maza.cewar kwamandan Hisbah.

Post a Comment

Previous Post Next Post