Innalillahi Kalli Irin Matsalar Da Shaye Shaye Ta Jefa Ƴan Mata Da Samarin Wannan Zaman

 A duk duniya a yau, babu inda ya kai arewacin Najeriya musamman jihar Kano, yawan masu shan Codeine, wani maganin tari mai sanya mutum bacci.

Masu bincike sun tabbatar wannan yana da alaka da halayyar jama’ar Arewa dake haifar wa da ‘yan mata da matan aure damuwa da rashin abin yi.

Matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi da kayan maye ta zama ruwan dare a arewacin Najeriya musamman a jihar Kano.

Bincike ya nuna lallai da yawan masu shan kayan mayen nan suna yi ne don su yaye wa kan su bakin ciki ko damuwa da suke tsintar kan su a ciki.

Sabon salon da ya fito, mata kuma ke yayi, shine shan Codeine da Rafanol da ma Benylin da sauran miyagun kwayoyi.

Post a Comment

Previous Post Next Post