Duk Namijin Da Ya Samu Mace Da Irin Wannan Halayen Zai Nace Har Sai Ya Aure Ta

 




Halaye da ɗabi'u na ƙwarai ke sa namiji yaji baya son ya rasa wacce yake son ya aura. Duk macen da take da waɗannan siffofin Maza na son su aure ta. Sai dai ba duka ne mata suke gane irin ɗabi'un da suke jawo hankalin maza zuwa gare su ba.


Shiyasa a wannan rubutun na yau muka kawo muku wasu daga cikin WaÉ—anan halayen da maza suke son suga duk macen da suke son yin rayuwa da ita ace tanada su. Sai dai ba duka mata ne suke da irin wannan siffofin ba, shiyasa muka yi wannan rubutun domin mata su koyi wannan halayen.


1: Macen da take da godiya duk Æ™anÆ™antar kyauta da za'a yi mata. Ba duka mata ne ke nuna godiyar su ba idan anyi musu Æ™aramar kyauta ba. Ita kyuta duk Æ™anÆ™artarta idan anyi miki yana da kyau ki nuna farin cikin ki da murna tare da yin godiya ga wanda yai miki wannan Kyautar. 


Namiji yana son idan yaiwa macen da yake so kyauta ta nuna farin ciki da godiya. Wasu matan suna da raina kyuta, koda kuwa babbar kyauta ce. Babu namijin da zai so kasance da matar da take raina kyauta.


2: Macen da ba tada ɓoye-ɓoye. Ko nuƙ-nuƙu.

Wasu matan sukan É“oye damuwar su ga mazajen da suke son auren su. Shi namiji yana son idan yana tare da macen da yake so tana faÉ—a masa damuwar ta. Kuma namiji baya son munafurci, yafi son duk abinda zaki karki É“oye masa.

Post a Comment

Previous Post Next Post