ABUJA: ‘Yan sandan sun kama matashin da ya rankwala wa mahaifin sa tabarya, ya yi sanadiyar rasuwar sa
Rundunar ‘yan sandan Babban Birnin Tarayyar Najeriya, Abuja ta bayuna cewa ta kama wani matashi mai shekara 16 bayan ya kashe mahaifinsa.
Kakakin rundunar Haruna Garba ya sanar da haka ranar Juma’a.
Garba ya ce matashin ya kashe mahaifinsa ne a ranar da ya ga Iyayen sa na dambe inda kawai cikin fushi sai ya dauki tabarya ya kwade mahaifinsa.
Ya ce wannan bugun da yaron ya yi ne ya yi ajalin mahaifinsa.
Garba ya ce rundunar za ta gurfanar da matashin a kotu 5da ake sauraren kararraki irin haka domin a gudanar da bincike akai.
Bayan haka kakakin rundunar ya ce fannin dake yaki da masu garkuwa da mutane ta ceto mutum 14 da akayi garkuwa da su inda a cikinsu akwai dagacen kauyen Chida dake gundumar Kwali a Abuja.