Kadan daga cikin anfanin kankana ajikin dan'adam



🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉

Kadan daga cikin anfanin kankana ajikin dan'adam


🍉 kankana na dauke da sinadarin dake samar da kariya da rage barazanar cutar hawan jini ga jikin bil'adama (Hypertension)


🍉 Kankana na taimakawa matuka wajen rage yawan kiba da nauyin jiki mai cutar da bil'adama.


🍉 Kankana na dauke da sinadarin “Glutathione” wanda ke taimakawa wajen kwarara garkuwar jikin bil'adama.


🍉 Kankana na dauke da sinadarin “Lycopene” wanda yake dagargaza kwayoyin cutar daji (Cancer)


🍉 Kankana na dauke da sinadarin (Vitamin C) wanda ke da tasiri wajen kashe kwayoyin cutar da ke cikin jinin bil'adama.


🍉 Kankana na dauke da sinadarin “Potassium” wanda ke taimaka wa zuciya, koda, Huhu da sauran muhimman sassan jikin bil'adama.


🍉 Kankana na samar wa fatan bil'adama kariya daga illolin da haske da tsananin zafin rana.


🍉 An bayyana masu shan Kankana da wadanda cutar Asthma za ta yi wuyar kama su saboda sinadarin Vitamin C da Kankana ke da shi. (Asthma prevention)


🍉 Kankana na taimaka wa jikin bil'adama wajen narkar da abinci cikin tsari.


🍉 Kankana na samar da kariya da rage barazanar cutar sugar ko Diabetes.


🍉 Kankana na samar da kariya ga cutar ciwon zuciya (Heart Attack).


🍉 Kankana na taimaka wa ma’aurata da kuzari da nishadi musamman a yayin gabatar da ibadan aure.

Post a Comment

Previous Post Next Post