WA YAFIKI SANIN SANIN SIRRIN MIJINKI


 ❀・・▼・・▼・・▼・・▼・・▼・❀

▼ ・WA YAFIKI SANIN SANIN SIRRIN MIJINKI ・▼

 □ S・R・M Islamic medical center □

      ◇ ⇢sirrin • rike • miji ⇢◇

✆ whatsApp

✁+2348037538596

✿www.sirrinrikemijinki@yahoo.com

✿www.Sirrinrikemiji@gmail.com

✎ D3C13938

Message Sirrin rike miji on WhatsApp. https://wa.me/message/2JY5R7B25CTJE1

▼▼▼▼▼

▼▼▼▼

▼▼▼

▼▼

✿━━━━━━━━━━━━━━━✿

        ♜・ GYARAN GASHI ・ ♜

▼▼▼

▼▼

Muddin uwargida na kokarin gyaran gashi lokaci

lokaci, za ta kiyaye gashin nata daga karairayewa,

zai rika laushi kuma ya kara tsawo. Domin cimma

wannan, za ki tanadi ganyen magarya, ki rika wanke

da shi, yana kara karfafa gashi ya kuma hana shi

zubewa. Ga wadansu daga cikin sinadaran da za ki

tanada:


1. Man zogale.

2. Man kwakwa.

3. Man zaitun.


Sai ki hade su guri guda ki rika shafawa a kanki a

matsayin man kitson ki, ko kuma ki tanadi:


1. Danyen kwai sabulun salo

2. Sabulun salo

3. Garin shammar


A fasa kwai, amma banda kwaiduwar farin kadai za

ki yi amfani da shi, sai ki zuba sabulun salo a ciki, ki

matse ki zuba garin shammar ciki sai ki wanke kai

da shi. Allah ya taimake mu.

Ga wani hadin kuma dai duk na gyaran gashi wannan

hadin na masu karamin karfi ne domin abubuwan da

za ki tanada ba za su fi karfin ki ba da farko za ki

tanadi ruwan Tumatur ne da sabulun salo kawai za ki

matse ruwan tumatir din sai ki zuba sabulun salon a

ciki ki barshin ya samu tsayin minti talatin idan ya

jika, sai ki shafa a kanki da dadare.

Idan zaki kwanta bacci, da safe sai ki sanya ruwan

dumi ki wanke tas. Insha Allah za ki ga gashinki ya

yi kyau sosai.


Wannan kuma man gashi ne mai sa laushin gashi da

tsawo ya yi baki yana shekin haske. Wannan hadin ba

zai taba barin gashin ki ya kare raye ba kuma zai rika

laushi sosai. Da farko zaki tanadi:


1. Zaitun shitta

2. Man alayyadi

3. Man zaitun

4. Man kwakwa

5. Man albasa

6. Man hulba

7. Man ridi


Za ku hada hulba da lalle gudaya sai ku tafasa, sai

ku tace ku wanke kai da shi, sannan ku hade dukan

wannan mayuka da na lissafo ku rinka shafawa a

kan ku zaku ga gashin ku yana kara kyau.


    ✎・   Gyaran Tafin Kafa・✎

❀━━━━━━━━━━━━━━━━❀

❀❀✿

✿❀

‘Yan’uwana mata yanzu zan yi bayyani ne a kan

yanda za mu kula da tafin kafanmu, ba ku b a zuwa

wajen wanke kafa, kawai za ku yi amfani da wannan

hadin kuma za ku ga abin mamaki. Ga ababen da za

ku tanada:


1. Man shanu

2. Man kwakwa

3. Man ridi

4. Man alayyadi


Zaku hade wanan mayukan gu daya, idan kafa tana

tsagewa ko tana kaushi, da daddare idan za ki

kwanta bacci sai ku shafa wannan mayukan a tafin

kafarku sai ku sami leda ku daure kafar da shi ku

kuma saka safa (socks) da safe ku wanke kafar da

ruwan dumi ku shafa man zaitun da man ridi. Ko

kuma ku nemi:


1. Man kwakwa

2. Man shanu

3. Man zaitun


Sai ku hade su gudaya suma kuringa shafawa da

dare kuma saka leda kuna daure kafar sannan kusa

sake safa (socks) idan gari ya waye ki fara gasa

kafar kadan sannan ki wanke da ruwan dumi, ki

shafa masa man zaitun.

Wannan hadin wanke kafa ne sai a tanadi:


1. Kokumba

2. Halle

3. Man ridi


Sai ku tanadi ‘Cucumber’ ku fere bayan ku yanyanka

shi kanana, a markada, amma fa kar a cika masa

ruwa domin an fi son ainihin ruwan ‘Cucumber’ din

sai a kwaba lallen da ruwan cucumber din, a rika

amfani da shi da dare, ana cirewa a wanke da safe,

ku kuma wanke kafar da ruwan dumi sai a shafawa

kafar man ridi insha Allah, indai aka rike wannan

hade-haden, za a ga amfaninsa, kuma za a yi

mamakin irin kyan da tafin kafar ku zai yi. Allah ya

taimakemu.


   ✿・  Rage kiba da tumbi・ ✿

❀❀❀

❀❀


Mata da dama ba su son kiba da tumbi, wannan

kuma ba komai yake jawo shi ba sai haihuwa da

wadansu matsalolin. Galibi, maza ba su cika son

masu kiba ko tumbi ba. Amma akwai hanyoyin

gyarawa. ‘Yan’uwa, za a iya gwada wannan hadin

domin biyan bukata:


1. Garin hulba

2. Ganyen na’a-na’a

3. Garin kanamfari

4. Zuma

5. Lemon tsami

6. Farin kwalli

7. Man na’a-na’a


Za a hade wadannan ganyen guri guda, a sa mi farin

kwalli dunkullale, za a saka a ciki, idan ya kai kamar

minti biyar sai a cire sannan a saka zuma a cikin

ruwan sai ku rika sha, shi kuma man na’a-na’a, za a

rika shafawa a tumbi ne zai ragu insha Allahu.


 Idan

kuma ana son rage kibar ne gaba daya sai a sa

lemon tsami a ruwan a rika sha.

Nan ma wani hadin ne na rage kiba za ku tanadi:


1. Habbatus-sauda

2. Sukari

3. Ganyen shayi dan aune

4. Zuma


Wannan hadin zaki hade su guri guda ku tafasa su ku

zuba zuma a ciki sai ku rinka sha.


✿━━━━━━━━━━━━━━━━━━✿

◇. GYARAN JIKI AMARE DA UWARGIDA ◇


Message Sirrin rike miji on WhatsApp. https://wa.me/message/2JY5R7B25CTJE1

✿✿✿

✿✿

⇢www.Sirrinrikemiji@gmail.com

⇢www.sirrinrikemijinki@yahoo.com

✎+2348037538596


Amfanin Garin Hulba Don Gyaran Jiki

Gyaran Fuska

▼▼▼

▼▼

Za ki samu garin hulbar ki dama da madara da

zuma ya damu sosai sai ki shafa a fuskar ki, ki

barshi kamar minti talatin kafin ki yi wanka, fuskar ki

zata yi sheki zai kashe miki pinplesya gyara miki

fuska kuma yana maida tsohuwa yarinya.


       ▼・Gyaran Gashi ・▼

▼▼▼

▼▼


Wato shi gashi wani abu ne wanda ke matukar

karawa mace kyau da kima shi yasa yake da kyau

mu dinga gyara gashin kanmu akai akai wato kuma

aduk abun gyara gashi ba kamar hulba, ga masu son

gashin su ya yi tsawo da sheki zaki hada garin hulba

coconut oil ki gauraya sosai sai ki shafa akanki ki

barshi yadadi akalla kamar, awa daya ko ma fiye da

hakan, kuma zaki ringa yin hakan kama sau biyu a

sati guda, sannan zaki kiyi na mako uku, yana kara

tsawon gashi, kuma gashin kanki zaiyi kyau da sheki,

kuma yana hana karyewar gashi.

Ga masu amosani, wato dandruff, zaki hada hulba

da apple cider ko ruwan khalki shafa a kanki, da san

dare ki barshi har gari ya waye, gabaki daya amosari

zasu mutu kuma gashin ki zai yi kyau.


  ▼・ Gyaran Cikowar Kirji ( NONO ) ・▼

Message Sirrin rike miji on WhatsApp. https://wa.me/message/2JY5R7B25CTJE1


▼▼▼

▼▼

Babu kamar hulba yana gyara sosai kuma yasa

kirjinki ya cicciko ya kara girma da kyau, wasu suna

zuba garin hulba ciki abinci kullum sunaci don

gyaran kirji in har abun ya zame masu jiki yana gyara

sosai, kuma bayan cikar kirji ma yana warkar da

cuttutuka da dama a jiki.

Haka kuma iya samun kindirmo mai kyau sai ku

hada da hulba kuma shay ana aiki biyu ne farko

gyaran kirji na biyu kuma sa ni’ima.

Ga wanda kirjin su ya kwan biyu suna iya hada garin

sa da kundirmo, sannan su sami mansa suna shan

spoon daya da safe daya da rana daya da marce,

bayan haka ma suna iya dafa garinsa su tace su sa

tsuma su gasa kirjin su da shi sannan kuma su hsafa

wa kirjin man sa.


Magana ta karshe anan  kuma abin fahimta, ba’aso

mace mai juna biyu ta sha hulba domin yana kawo

nakuda da gagawa. Na biyu mata masu shayarwa

suna iya hada garin hulban a cikin abincin su yana

kara nagartaccen ruwan mama, kuma zai sa jinjiri ya

kasance cikin koshin lafiya.

Karin Bayani Game Da Karin Ni’imar Mace

Kamar yadda muka sha yin bayani a baya dangane

da karin ni’ima a jikin mace, har kullum muna dada

fadada wannan bangaren, inda a kullum masana

harkar kiwon lafiya ke gudanar da karin haske kan

wannan batu.


Uwargida za ki iya samun sassaken Baure, ki dafa

shi sai bayan ya dafu sai ki juye ruwan sai ki samu

mazarkwaila da zuma da kanunfari da citta, ki zuba

aciki, ki tafasa ki rika sha safe da yamma.


Masana tun tabbatar da cewa dukkanin macen da ke

amfani da wannan, za ta samu karin ni’ima a jikinta,

sannan ta kasance mai dimbin alheri ga maigidanta.

Bayan haka, za ki iya samun totuwar rake mai

tsafta, sai ki bar shi ya bushe, ki samu Bagaruwa

guda uku da Almuski da Kanumfari, ki hada su, waje

daya ki rika tsuguno kuma ki rika goga zaitun a jiki,

musamman a gabanki, hakan zai kara miki ni’ima

mai yawae.

Bayan wannan, za ki iya samun RIDI, ki wanke shi,

ki nika har sai ya zama gari, ki bar shi, ya bushe, ki

rika sha da nono, zai kara miki ni’ima gasken-gaske,

musamman wajen ibadar aure. Haka kuma yana

maganin dattin mahaifa. Dangane da masu neman

karin girman mama da sauransu…? A kullum na kan

yi kokarin bayyana musu wasu irin sinadaran da za

su yi amfani da shi, amma kuma suna bukatar karin

bayani. Abin sani shi ne wasu matan daga sun yi

haihuwa daya, za ka ga nononsu ya zube, wannan

yana saka maigida, musamman irin mazan da suke

son ganin mace da cikar mama cikin damuwa, wasu

ma sai ya haifar musu da neman sabon aure.


Don haka uwargida, ki samu Habbatus-Sauda, Hulba,

Alkama, Gyada, Ridi, Danyar shinkafa da Busassen

Karas, duk ki daka su waje daya, kina sha da

madarar ruwa na gwangwani, misali PEAK. Kina iya

sha sa’o’i biyu akalla kafin barci da kuma Sa’o’i biyu

bayan kin farka daga barcin.

▼▼▼▼▼▼

▼▼▼▼▼

www.sirrinrikemijinki@yahoo.com

www.Sirrinrikemiji@gmail.com

✯✎+2348037538596

✿・・・・・・・・・・・・・・・・✿

Copyright BY: Sirrin rike miji

FACEBOOK GROUP: sirrin rike miji

EMAIL: sirrinrikemiji@gmail.com

FACEBOOK PAGE LIKE: sirrin rike miji

WhatsApp: ☏+2348037538596


Message Sirrin rike miji on WhatsApp. https://wa.me/message/2JY5R7B25CTJE1

Post a Comment

Previous Post Next Post