Yar Haya Ta Kashe Mai Gida Ta Hanyar Matse 'Ya'yan Marainansa A Ogun Talata, Maris 14, 2023 at 2:09 Yamma daga Aminu Ibrahim Wata yar haya ta kashe mai gidan da ta ke haya har lahira ta hanyar jan mazakutarsa biyo bayan hatsaniya Mamacin ya fadi bayan matar ta ja mazakutarsa inda aka garzaya da mamacin asibiti inda likita ya tabbatar da mutuwarsa Jami'an yan sanda sun cafke wacce ake zargin Ifeoma Ossai, tare da alkawarin fada bincike da kuma gurfanar da ita DUBA NAN: Danna “See First” karkashin karkashin "Following “ don samun labaran Legit.ng a shafinka na Facebook akai-akai Ogun- Jami'an yan sandan Jihar Ogun sun kama wata mata mai shekaru 33, Ifeoma Ossai, bisa zargin kashe maigidan da ta ke haya dan shekara 50, Monday Surulere Oladele, saboda wata karamar hatsaniya. Wakilin Daily Trust ya ruwaito cewa wadda ake zargin ta shiga hannu biyo bayan rahoton da aka shigar a ofishin Sango Ota ta hannun wani Olaleye Taiwo. Yar haya da ake zargin ta kashe mai gidan haya. Hoto: Daily Trust Read more:
