Mutumin da yayi lalata da ‘Yarsa’ ‘yar shekara 7 ya gurfana gaban kotu
Kotu ta tasa ƙeyar wani magidanci da yayi lalata da ‘yarsa ya shekara 7 zuwa gidan yari
Wata kotun majestari mai lamba biyu dake da zama a unguwar Iyaganku a birnin Badun na jihar Oyo ta bada umarnin tsare wani magidanci a gidan gyaran hali sakamakon zargin sa da yin lalata da ‘yarsa ‘yar shekara 7.
Mutumin mai suna Gboyega lasisi ɗan shekara 50 ana zarginsa da lalata kankanuwar ‘yarsa ta cikinsa.
Alkalin kotun mai shari’a P.O Adetuyibi nan take ya bada umarnin tsare mutumin a gidan yari dake Abolongo a birnin Oyo.
