Qalu Innalillahi mutuwa kenan Daliba mai makin karatu na karshe zanso kowa ya shiga yaji abun da yafaru…

 

Qalu Innalillahi mutuwa kenan Daliba mai makin karatu na karshe zanso kowa ya shiga yaji abun da yafaru…


Jihar Yobe – Wata É—alibar jami’ar jihar Yobe (YSU), Maryam Lawan Goroma, ta riga mu gidan gaskiya jim kaÉ—an bayan ta kammala rubuta jarabawa.

Jaridar Leadership ta tattaro cewa Maryam ta faÉ—i ne a ranar Alhamis, 27 ga watan Afirilun 2023, sannan aka wuce da ita zuwa asibiti inda aka tabbatar da cewa ta rasu.

Wani ɗan ajin su mai suna Mallam Bukar Maisandari, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya bayyana cewa, lafiyar Maryam ƙalau kafin rasuwar ta, cewar rahoton Punch.

Inna Lillaahi Wa Innaa Ilaihir Raji’un. Yanzu cikin baĆ™in ciki na ke samu labarin rasuwar Ć´ar ajin mu, Maryam Lawan Goroma.”

“Tana cikin Ć™oshin lafiya har zuwa yau da rana lokacin da ta faÉ—i inda jim kaÉ—an aka tabbatar ta rasu. Allah ubangiji ya yafe mata kurakuran ta. Allah ya sanya Aljannah Firdausi ta zama makoma a gare ta. Ina miĆ™a ta’aziyya ta ga Ć´an’uwa da abokai da dukkanin Ć´an ajin mu. Allah ya ba ku haĆ™urin jure wannan babban rashin. Ameen.”

Post a Comment

Previous Post Next Post