Ɗalibi ya daɓa wa malamarsa wuƙa har lahira

 Ɗalibi ya daɓa wa malamarsa wuƙa har lahira

Danna domin ganin video 👇


Wani ɗalibin makarantar sakandare ya ɗaba wa wata malama yar ƙasar Sifaniya wuƙa har lahira a wata makaranta a garin Saint-Jean-de-Luz na ƙasar Faransa.

Ɗan sanda mai shigar da ƙara na yankin, Jerome Bourrier ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na AFP harin, inda kafafen yaɗa labaran ƙasar suka ce lamarin ya faru ne a cikin aji a safiyar ranar Talata.

Hukumomi sun tabbatar da cewa ‘yan sanda suna wurin tare da mai gabatar da ƙara na yankin.

Rahotanni sun ruwaito cewa an kama ɗalibin.

Malamar tana da shekaru hamsin kuma ta mutu sakamakon bugun zuciya lokacin da jami’an agajin gaggawa suka isa wurin, kamar yadda kafafen yada labaran ƙasar suka bayyana.

Kafafen yaɗa labarai sun ruwaito cewa akwai alamu da ke nuna cewa ɗalibin yana fama da matsalar kwakwalwa.

Sun ce a binciken da suka gudanar kawo yanzu, babu alamu da suka nuna cewa harin na da alaƙa da ta'addanci.

Post a Comment

Previous Post Next Post