Girkin tuwon masara miyar ayayo da kubewa:


 Girkin tuwon masara miyar ayayo da kubewa:


GIRKE GIRKE

 


AMINA ABDULLAHI


Assalamu alaikum uwargida, barkanmu da sake haduwa da ku a wannan fili namu na girke-girke.


A yau na kawo muku yadda ake girka tuwon masara da miyar ayayo da kubewa domin ya kamata mu koma girkin gargajiya kada maigida ya gaji da yawan cin girkin zamani.


Yana da kyau mace ta kware a kowane irin girki. Ta zamo a ko’ina ma tana da ilimin wannan girkin, in har maigida ya saba da cin nau’o’in girke-girkenta, zai wuya ya je unguwa ya ci abinci.


Koda tafiya ya yi zai ji ya kosa ya dawo domin cin tuwon uwargida.


Abubuwan da za a bukata:


Garin masara

Ganyen ayayo

Kubewa danya

Albasa

Attarugu

Sunadarin Dandano

Nama

Tafarnuwa

Man shanu

Yadda ake yin hadin: A kai masara injin nika sai a surfa ta, sannan a nika ta yi laushi.


Bayan haka, sai a tankade ta a ajiye a gefe.


Sannan a dora ruwa a kan wuta. Idan ya tafasa sai a debi gari kadan a zuba a ruwa a kada shi sannan a juye a tafasashen ruwan a kan wutar; wannan ake kira talge.


Sai a rufe tukunyar da marufi na tsawon lokaci har talgen ya nuna.


Sai a sake debo garin ana zubawa ana tukawa har ya dan yi tauri sannan a sake mayar da marufin a rufe.


A wanke kubewa danya sannan a yanka ta kanana a zuba a turmi da ’yar kanwa a jajjaga ta sosai har sai ta jajjagu.


Bayan haka sai a kwashe a ajiye a gefe. A tsintsinke ayayo sannan a yayyanka shi kananan sannan a wanke da ruwan gishiri shi ma a wanke a ajiye a gefe.


Bayan haka, sai a jajjaga albasa da attarugu a ajiye su ma a gefe.


A tafasa nama, bayan ya nuna sai a kara ruwa a zuba jajjagen albasa da attarugun a ruwan da manja da jajjagen tafarnuwa su tafasa sosai.


Sannan a dauko jajjagen kubewa da yankakken ganyen ayayon a zuba.


Za a ga miyar ta fara kumfa da yauki.


Haka za a rika gaurayawa har sai miyar ta hadu sannan sai a zuba sunadarin dandano.


Sai a dauko tuwon masarar a zuba masa wannan miya a kai tare da diga mata man shanu.


A yi santi lafiya!


SHARES

Post a Comment

Previous Post Next Post