Baban Chinedu ya bayyana wadanda suka kona gidan Rarara ba yan Kwankwasiyya bane

 

Baban Chinedu ya bayyana wadanda suka kona gidan Rarara ba yan Kwankwasiyya bane


Bayan kone-kone da Hasara da Jarumin Fina-finai da Wakokin Hausa a Masana’antar Kannywood, Baban Chinedu da kuma abokinsa mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara suka tafka, Mutane da dama sun cigaba da yada zarge-zarge akan cewa Magoya bayan Kwankwaso yan Kwankwasiyya sune suka aikata Wannan aika-aika.

Masu yada jita-jitar sunce Dalilin da yasa Suke zargin yan Kwankwasiyya dayiwa Rarara wannan barna shine saboda Sun dade suna hakuri da Rarara Sakamakon cin mutuncin da ya dade yana musu na Wakoki yana zagin masu gidan su da kuma manya da Dattijai, wannan ne yasa suke ganin cewa yan Kwankwasiyya ne sukayi hakan.

Sai dai Kuma, Baban Chinedu Wanda yake shine na hannun dama a gurin Dauda Kahutu Rarara, ya bayyana cewa wadanda sukayi wannan aika-aikar ba yan Kwankwasiyya bane.

Post a Comment

Previous Post Next Post