Wata al’adar da wasu mutane ke yi ya yin da aka ɗaura auren budurwa a yankinsu ta bukatar gwajin budurci daga amarya da kuma karfin iyawa daga ango wanda za a gwada shi da goggon amarya.
Al’ummar Banyakole a ƙasar Uganda suna da wata Al’ada wacce idan za a miki aure tilas ne gwogginki ta zama miki babbar ƙawa saboda ƙauna da soyayya da kuma jagorantar ƴar uwarta ta hanyar zama aminiya ga ƴar yayarta musamman kan abubuwan da ba za ta iya rabawa da mahaifiyarta ba.
Domin a wajen ƙabilar Banyakole na Uganda, aikin inna ya wuce yin nasiha kawai har ma da ɗaukar duk wani nauyi da ya gagari amarya ta yi shi tare da mahaifiyarta a al’adance.
Mutanen Banyakole wadanda kuma ake kira da kabilar Ankole mazauna Masarautar Bantu ce wacce ta samo asali tun daga karni na 15. Tana cikin Kudu maso Yammacin Uganda, gabas da Tafkin Edward, masarautar da Sarki Mugabe ke mulki wacce ta shahara da kare haƙƙin aure na musamman.
Auren Banyakole
Aure a cikin wannan al’ada yana da mahimmancin gaske yayin da iyaye ke samun farin ciki da alfahari daga auren ƴaƴansu. A bisa al’adar Banyakole, idan yarinya ta kai shekara takwas ko tara, aikin inna ne ta gyara ta don rayuwar iyali. Gwoggon ta za ta koya mata duk wani abu daya kamata ta sani game da matsayinta na mace mafi mahimmanci, a matsayin matar aure.
