ANA HASASHEN RIKICI A ZABEN GWAMNONI


 ANA HASASHEN RIKICI A ZABEN GWAMNONI


Na bibiyi bayanai da rahoton tsaro akan zaben Gwamnoni da za'a gabatar ranar asabar mai zuwa idan Allah Ya kaimu


Bahasin tsaro ya bayyana jihar Kano, Lagos, Katsina, Zamfara, Bauchi, Kaduna, Sokoto da Borno a matsayin jihohin da ake hasashen za'a samu tashin hankali sosai fiye da sauran jihohin


A bangaren hukumomin tsaro, yanzu haka daga Abuja an tura kwararrun jami'an tsaro zuwa wadannan jihohi da na ambata domin suyi abinda ya dace


Zanyi amfani da wannan damar domin na ja hankalin 'yan uwana matasa Musulmai, ku sani jami'an tsaro sun shirya, kuma suna da order na harbin duk wanda yace zai kawo cikas lokacin zabe Wallahi, ina wannan maganar ne da hujja bisa abinda na gani a zahiri


Dan uwa Kar ka yadda ka mutu a kan siyasar Demokaradiyyah, ka sani Demokaradiyyah ba tsarin Musulunci bane, ana yinta bisa lalura ne kawai, kar ka yadda ko yatsa ka nuna wa dan uwanka Musulmi akan wannan siyasa ta Demokaradiyyah balle ka dauki makami ka cutar da shi


Malam ko a filin jihadi don daukaka kalmar Allah aka kasheka baka da garanti akan samun shahada har sai ka tsarkake niyya kayi don Allah ba don mutane su ce kai jarumi bane, balle wata shirme Demokaradiyyah da take fada da Musulunci 


Ka sani cewa rayuwar duniya ba itace rayuwa na tabbas ba, kar ka yadda kayi karshen rayuwar duniya a hanyar banza, saboda Allah Madaukakin Sarki Zai tashi kowa ranar Alkiyama akan hanyar da ya mutu


Matasa ku waye, kuyi hankali, 'yan siyasa da zasu turaku aikata ta'addanci lokacin zabe ku kallesu da kyau babu 'ya'yansu a ciki, saboda suna son 'ya'yansu, don haka 'yan siyasa da zasu turaku aikata laifi lokacin zabe inda zaku iya rasa ranku a aikin banza to ba masoyanku bane, sune cikakkun makiyanku


'Yan uwa masu albarka ku taimaka wajen yada wannan sakon zuwa ga inda ya dace


Muna rokon Allah don Tsarkin MulkinSa Ya sa ayi wannan zabe lafiya a kammala lafiya.

Dukkan hasashe na tashin hankali da ake tsammanin zai faru lokacin zabe Allah Ya kawar mana dashi.


Post a Comment

Previous Post Next Post