WANNAN LABARIN ABUN ALFAHARI NE GA DUK WANI MUSULMI





 


 WANNAN LABARIN ABUN ALFAHARI NE GA DUK WANI MUSULMI: 

Nan bada dadewa ba gaba daya Duniya zata zama kasar musulunci.

Inji - Babban Paston Cocin kasar Rasha


Acewar shugaban cocin Rasha, Kasashen Turai irin su kasar Rasha da sauran Kasashen yammacin Turai duk sun fara zama kasar musulunci, saboda a kasar Jamus Kashi 

30% cikin dari na kiristocin kasar duk tsofaffine. Hakan yasa kashi 70% na matasa masu jini a jika na Jama'ar kasar zasu zama musulmi Nan bada dadewa ba.


Paston yaci gaba da cewa, akasar shi ta Rasha, kiristoci suna cike filayen kwallo da gidanjen rawar Disco, amma a ranakun lahadi sai kaga babu  kowa a coci. Amma a gefe daya musulmai suna cika masallatai don gunar da ibada. 


 Abun mamaki ne yadda dubban musulmi sukeyin dandazo a manyan filayen wasanni don gudanar da sallalolin idi, wannan ba karamin abun mamaki bane.


Duk inda ka shiga a kasar Ingila, zakaji Ana ta ambaton sunan annabi Muhammad. 


Sannan a halin yanzu Kaso 49% na mazauna birnin Brussels duk Muslmi ne. Don haka nake Kara jaddadawa nan bada jimawa ba duk Duniya zata zama kasar musulunci.


Daga Abdullahi Adamu

Post a Comment

Previous Post Next Post