Yanda ake Miyar Kabeji Mai Nama.


Yanda ake Miyar Kabeji Mai Nama.

yadda ake miyar kabeji mai nama. Wannan irin miya tana kara lafiya a jiki sannan tana da dadi idan aka hada ta da farar shinkafa ko da dafaffiyar doya da kuma farar taliya da sauransu. Yana da kyau uwargida ta koyi yadda za ta rika canza dandanon miyarta a koda yaushe. Samun canji a dandanon girki na da alaka da irin kalar magi da kuma kayan kanshin da ake sa wa a lokacin girkin.




Abubuwan da za a bukata

- Kabeji

- Nama

- Man gyada

- Attarugu

- Albasa

- Tumatir

- Maggi

- Kori

- Tafarnuwa



Yanda Ake hadawa;

Da farko za a samu kabeji sannan a yayyanka  manya-manya sannan a wanke da ruwan gishiri domin kashe kowace irin kwayar cuta da ke ciki sannan a yayyanka albasa da tumatir kwaya biyu kacal sannan a jajjaga attarugu da tafarnuwa.





Daga nan sai  wanke nama sannan a silala da albasa da gishiri kadan bayan ta yi laushi, sai a yayyanka kanana sannan a soya sama-sama. Bayan haka, a dora tukunya a wuta, a zuba man gyada kadan sannan a zuba albasa da tumatir da kuma jajjagen attarugu da tafarnuwa a soya.

 

Post a Comment

Previous Post Next Post